Labarai
INEC ta fara gudanar da zaɓen gwaji a Kano.

Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) ta fara gudanar da zaɓen gwaji a jihar Kano, domin gwada shirye-shiryenta da tsarin gudanar da zaɓe gabanin zaɓukan da ke tafe na 2027.
Shugaban INEC, na Kano, Ambasada Abdu Zango, ne ya bayyana hakan a yayin zagayen duba cibiyoyin da ake gudanar da zaɓen gwajin, inda ya yaba da yadda ake gudanar da aikin.
Zango ya kuma gargaɗi magoya bayan jam’iyyun siyasa da su guji zuwa wuraren zaɓe da tambarin jam’iyyunsu, yana mai cewa hukumar ba za ta lamunci yin hakan ba.
Hukumar ta kuma ce za ta yi aiki kafaɗa da kafaɗa da jami’an tsaro domin tabbatar da gudanar da zaɓe cikin gaskiya, adalci da inganci, yayin da wasu daga cikin masu zaɓen gwaji suka bayyana ra’ayoyinsu kan yadda aka gudanar da aikin.
A wasu guraren zaɓen gwajin dai an samu karancin fitowar mutane, inda wasu daga cikin jami'an hukumar suka makara wajen zuwa gurin zaɓen gwajin, ko da ike a mafi yawan rumfunan zaɓen an samu zuwa jimai'an da wuri.


