Dala FM
Muryar Jama'a
Yanzu-yanzu
Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa ta buƙaci matasa su tashi tsaye wajen samar wa yankunan su ci gaba.Gwamnatin Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na yau Asabar.Gwamnatin Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na yau Asabar a jihar.Hukumar Shari'a ta jagoranci buɗe sabon masallacin juma'a a garin Tiga dake Kano.Kwankwaso ya zargi Gwamna Abba da amfani da hukumomin yaƙi cin hanci da rashawa wajen yaƙar sa a siyasance.Hukumar Shari'a ta buƙaci gudunmawar masu jaridun internet don daƙile kalaman cin mutunci a Kano.Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa ta buƙaci matasa su tashi tsaye wajen samar wa yankunan su ci gaba.Gwamnatin Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na yau Asabar.Gwamnatin Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na yau Asabar a jihar.Hukumar Shari'a ta jagoranci buɗe sabon masallacin juma'a a garin Tiga dake Kano.Kwankwaso ya zargi Gwamna Abba da amfani da hukumomin yaƙi cin hanci da rashawa wajen yaƙar sa a siyasance.Hukumar Shari'a ta buƙaci gudunmawar masu jaridun internet don daƙile kalaman cin mutunci a Kano.
← Labarai
Labarai

Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa ta buƙaci matasa su tashi tsaye wajen samar wa yankunan su ci gaba.

Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewacin Najeriya, ta buƙaci matasa da su tashi tsaye tare da cire tsoro wajen nema wa yankunan su ci gaban da ya dace, domin cin moriyar shugabannin da suke wakiltar su a matakai daban-daban.

Shugaban Gamayyar Matasan Arewan, Kwamared Muhammad Tijjani Ɗorayi (MTD) ne ya bayyana hakan a yayin taron ƙungiyar ci gaban Ɗorayi Chiranci, da ya gudana da safiyar ranar Asabar 28 ga watan Nuwamba, 2026.

Ya ce duba da yadda mafi yawan al'umma ke bukatar tallafi mahukunta ta ɓangaren al'amuran more rayuwa, a don haka akwai buƙatar matasan su ƙara dagewa wajen nemar wa yankunan nasu ci gaban da ya dace.

Muhammad Tijjani MTD ta kuma buƙaci ƴan ƙungiyar ta ci gaban Ɗorayi Chiranci da su ƙara ruɓanya ƙokarin su wajen tinkarar shugabannin yankin su domin ganin sun kawo musu ɗauki kan matsalar tsaro da sauran ɓangarori.

Ya kuma yi kira ga iyaye da su bada gudunmawar su wajen kula da tarbiyyar ƴaƴansu tare da tsawatar musu kan gujewa shiga harkokin faɗan daba, da shaye-shayen kayan maye, da sauran miyagun ayyuka.

Ya kuma yi alƙawarin tallafa wa ƙungiyar da dukkanin abinda ya sawwaƙa, kuma ciki har da sanya ƙungiyar a cikin tallafin da suke bayarwa domin samar da ci gaban matasan yankin.

Da yake nasa jawabin, Shugaban Ƙungiyar samar da ci gaban Ɗorayi Chiranci, Musa Ahmad Yusuf, ya ce sun samar da ƙungiyar ne domin haɗin kan matasa tare da nemar wa yankunan su ci gaban da ya dace.

A cewar sa, sun shirya tinkarar shugabannin yankunan su a siyasa, domin sanar musu matsalolin da suke addabar al'ummar yankunan don ganin an kai musu ɗaukin da ya dace.

A yayin taron, al'umma da dama ne suka samu damar halarta, kuma ciki har da Mai unguwar Chiranchi Yamma, Mallam Nura Abdullahi, da mai unguwar Chiranci Gabas, Malam Shehu Iliyasu, da Shugaban Gamayyar Kwamitocin tsaro na yankin Ɗorayi, Malam Abdullahi Idris Ɗan fodiyo, ƴan siyasa, malamai da dai sauran su.

Dala FM Kano 88.5 FM
Dala FM Kano 88.5 FM · Kai tsaye
Live