Labarai
Gwamnatin Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na yau Asabar a jihar.

Gwamnatin Jihar Kano ta sanar da dakatar da aikin tsaftar muhalli na yau Asabar, saboda zaɓen gwaji da Hukumar Zaɓe ta Ƙasa (INEC) za ta gudanar.
Kwamishinan Muhalli da Sauyin Yanayi na Kano, Alhaji Hamza Safiyanu Kachako, ne ya sanar da hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a daren jiya Juma'a 27 ga watan Nuwamba, 2026.
Sanarwar ta ce an ɗauki wannan mataki ne domin bada damar gudanar da zaɓen gwajin cikin sauƙi, tare da tabbatar da cewa jama’a ba su fuskanci tangarɗa wajen gudanar da ayyukansu ba.
Gwamnatin Kano ta buƙaci al’umma su lura da sanarwar, tare da ci gaba da kula da tsaftar muhalli a gidajensu da wuraren da suke gudanar da harkokinsu.


