Labarai
Hukumar Shari'a ta buƙaci gudunmawar masu jaridun internet don daƙile kalaman cin mutunci a Kano.

Hukumar Shari’a ta Jihar Kano, ta yi kira da a ƙarfafa haɗin gwiwa da masu aikin jarida na kafafen yaɗa labarai na internet, domin magance amfani da kafafen sada zumunta ta hanyar da ba ta dace ba.
Cikin abubuwan da hukumar ke son a daƙile a ɓangaren, akwai yaɗa kalaman cin mutunci, tayar da zaune tsaye kan addini, da gaba da juna a siyasa da sauran abubuwan da ka iya lalata tarbiyya da ɗabi’un al’umma.
Kwamishina na biyu a Hukumar, Sheikh Ali Danabba ne ya buƙaci hakan a yayin wani taro na musamman da hukumar ta gudanar tare da mambobin Ƙungiyar ’Yan Jarida masu wallafa labarai a internet, ta Kano (KOMC), ranar Alhamis 26 ga Nuwamba, 2026, a hedikwatar hukumar da ke Kano.
Taron ya ba hukumar damar jan hankalin masu gudanar da kafafen yaɗa labarai na internet, kan yadda kafafen ke ƙara yin tasiri wajen tsara tunanin al’umma, fahimtar addini da tattaunawar siyasa, musamman a jihar Kano, inda addini da al’adu ke da muhimmiyar rawa a rayuwar yau da kullum.
Shiekh Danabba ya jaddada cewa, kafafen yaɗa labarai bai kamata su tsaya kawai wajen yaɗa labarai ba, a maimakon haka, ya kamata su kasance hanyoyin inganta ɗabi’a, zaman lafiya da kiyaye kyawawan al’adun da aka san jihar Kano da su tsawon lokaci.
A cewar sa, ɗaya daga cikin abubuwan da suka fi damun hukumar shi ne yadda wasu masu amfani da kafafen sada zumunta ke amfani da addini domin cimma muradun siyasa, cin mutuncin mutane, yaɗa kalaman da ke tayar da hankali da kuma mayar da martabar addini wata hanya ta haddasa rarrabuwar kawuna.
Ya bayyana cewa masu aikin jarida na yanar gizo suna da muhimmiyar rawar da za su taka wajen sauya wannan yanayi, ta hanyar bin ƙa’idojin aikin jarida, guje wa yaɗa kalaman tunzura jama’a da kuma tabbatar da cewa kafafensu ba su zama hanyoyin yaɗa batsa, labaran ƙarya da ɓata sunan mutane ba.
Da yake mayar da martani kan batutuwan da hukumar ta gabatar, shugaban Ƙungiyar ’Yan Jarida Masu aiki a internet, ta Kano, Comrade Abubakar Abdulkadir Dangambo, ya yi tsokaci kan batutuwan da aka gabatar.
Ya kuma jaddada muhimmancin ƙwarewa, riƙon amana da bin ƙa’idojin aikin jarida a harkokin yaɗa labarai na dijital, musamman a wannan lokaci da saƙonnin da ake wallafawa a kafafen sada zumunta ke yaɗuwa cikin sauri, tare da yin tasiri ga ra’ayin jama’a tun kafin a tabbatar da sahihancinsu.
Taron ya samar da wata dama ga Hukumar Shari’a da Ƙungiyar ‘Yan Jarida Masu Aikin Yanar Gizo, wajen gina kyakkyawar alaƙar aiki ta hanyar tattaunawa akai-akai, wayar da kan jama’a da shirye-shiryen da za su taimaka wajen hana amfani da addini da kafafen sada zumunta ta hanyar da ba ta dace ba.


