Labarai
An sake tsintar wani Jariri sabuwar haihuwa a Ƙofar Na'isa da ke Kano.

Rahotanni sun bayyana cewa an sake samun wani jariri a unguwar Kofar Na’isa da ke cikin birnin Kano, ƙasa da kwanaki biyu bayan samun rahoton tsintar wasu jarirai ƴan tagwaye biyu a unguwar Dorayi Unguwar Bello, da ke Ƙaramar hukumar Gwale a Kano.
Ɗan gwagwarmayar nan Comrade Umar Hamisu Kofar Na’isa, ne ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya ce an samu jaririn ne da misalin ƙarfe 7:00 na safiyar yau Litinin 23 ga watan Nuwamba, 2026.
A cewarsa, wani yaro ne ya buɗe wata leda da aka ajiye a wurin, inda ya tarar da jaririn sai dai ana kyautata zaton cewar jaririn ya rasu.
Sai dai ya ce kawo yanzu ba a kama waɗanda suka ajiye jaririn ba.
Ƴan tagwayen jariran da aka tsinta a yankin Ɗorayi, yanzu haka an tabbatar da rasuwa ɗaya daga cikin su.
Lamarin ya ƙara tayar da hankalin al'umma kan yadda ake samun rahotannin ajiye jarirai a wasu sassan birnin Kano.


