Labarai
Saboda a raba ni da mata ta har gida aka zo aka kwashe kayan ta, aka yi garkuwa da ita - Gwamnan Kano

Gwamnan jihar Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ya ce saboda a raba shi da matar sa har gida aka zo aka kwashe kayan ta, aka yi garkuwa da ita.
Gwamnan ya bayyana hakan ne a lokacin da yake tattaunawa da BBC Hausa, kan lamarin da ya faru a tsakanin sa da matar sa wanda ya yi sanadiyyar sakin ta a bainar jama'a a makon da ya gabata.
Abba Kabir Yusuf, ya kuma yuna takaicin sa kan yadda aka biyo masa ta hanyar shigar dashi ƙara a gaban kotu a Abuja, yana mai fayyace cewa, al'amarin aure ba abu bane mai sauƙi abu ne mai matuƙar wahala.
Abba ya kuma ce yana ci gaba da bibiyar lamarin bisa ga sasancin kotu har zuwa lokacin da za a warware lamarin da ya shafi tsakanin sa da matar sa.
Abba ya ce yana da cikakkun bayanai da shaidu kan yadda lamarin ya faru, amma bai ga dacewar bayyana dukkan bayanan a bainar jama'a ba.
Ya ce duk da abubuwan da suka faru, ya zaɓi yin shiru na tsawon lokaci domin kaucewa fito da al'amuran gidansa fili.
Da aka tambaye shi dalilin da ya sa ya yi magana kan lamarin a bainar jama'a, gwamnan ya mayar da martani cewa ba shi ne ya mayar da batun siyasa ba, su ne suka fara hakan.


