Labarai
An tsinci ƴan tagwayen jarirai sabuwar haihuwa a yankin Ɗorayi da ke Kano.

Mazauna layin Gidan Takwas da ke yankin Ɗorayi unguwar Bello a ƙaramar hukumar Gwale ta jihar Kano, sun wayi gari da ganin wasu ƴan tagwayen jarirai sabuwar haihuwa da aka ajiye su aka tafi aka bar su.
Wata daga cikin mazauna yankin da ta nemi a sakaye sunan ta ce ta shaidawa Dala FM Kano, faruwar lamarin a ranar Lahadi 22 ga watan Nuwamba, 2026.
Ta ce an ajiye ƴan tagwayen jariran ne da misalin ƙarfe 11:00 na daren ranar Asabar 21 ga watan Nuwamba, 2026.
Sai dai ta ce har zuwa wayewar garin ranar Lahadi, ba a iya gano waɗanda suka ajiye jariran biyu ba.
A cewar matar, lokacin da suka tsinci ƴan biyun babu kaya a jikin su, daga bisani ne al'umma suka taimaka aka samo kaya inda aka sanya musu, kuma aka kai su gidan mai unguwa mafi kusa.
Ta ce sun matuƙar shiga cikin tashin hankali hankali kan yadda suka tsinci ƴan tagwayen, kasancewar ba su taɓa cin karo da irin wannan lamari ba.


