Dala FM
Muryar Jama'a
Yanzu-yanzu
Kotu ta aike da Abubakar Uran gidan yari bisa zargin satar wayar wutar lantarki a Kano.Masarautar Gumel ta haramta ɗaukar hotuna da Bidiyo a fadar sarki ba tare da izini ba.El-rufa'i ya musanta zargin sauraron wayar Nuhu Ribadu a Kotu.Ma'aikacin Kanawa Radio Kano, Umar Tijjani Sabi'u (No Time) ya rasu.Kwankwaso ya musanta aike Gwamna Abba Yusuf zuwa wajen Tinubu don tattaunawa kan komawarsu APC.Hukumar Shari'a ta sulhunta ƴan siyasar da ke jifan juna da munanan kalamai a Kano.Kotu ta aike da Abubakar Uran gidan yari bisa zargin satar wayar wutar lantarki a Kano.Masarautar Gumel ta haramta ɗaukar hotuna da Bidiyo a fadar sarki ba tare da izini ba.El-rufa'i ya musanta zargin sauraron wayar Nuhu Ribadu a Kotu.Ma'aikacin Kanawa Radio Kano, Umar Tijjani Sabi'u (No Time) ya rasu.Kwankwaso ya musanta aike Gwamna Abba Yusuf zuwa wajen Tinubu don tattaunawa kan komawarsu APC.Hukumar Shari'a ta sulhunta ƴan siyasar da ke jifan juna da munanan kalamai a Kano.
← Labarai
Labarai

El-rufa'i ya musanta zargin sauraron wayar Nuhu Ribadu a Kotu.

Tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, ya musanta zargin cewa ya shiga cikin sauraron tattaunawar wayar tarho ta Mai Bai wa Shugaban Ƙasa Shawara kan Harkokin Tsaro, Nuhu Ribadu, ko kuma ya umarci wani da ya yi hakan.

El-Rufai ya bayyana hakan ne a ranar Laraba, inda ya ƙaryata zargin da ake masa kan lamarin.

A baya dai, an samu ce-ce-ku-ce bayan kalaman da El-Rufai ya yi a wata hira da gidan talabijin na Arise, inda ya ce an saurari wata tattaunawa ta wayar Ribadu, wadda a cewarsa ta shafi umarnin kama shi.

Lamarin ya jawo martani daga wasu jami’an gwamnati, sannan Hukumar DSS ta shigar da ƙara a kansa bisa zargin sa hannun sa wajen kutse da sauraron tattaunawar wayar NSA.

Sai dai El-Rufai ya ci gaba da musanta zargin da ake masa.

Dala FM Kano 88.5 FM
Dala FM Kano 88.5 FM · Kai tsaye
Live