Dala FM
Muryar Jama'a
Yanzu-yanzu
Kotu ta aike da Abubakar Uran gidan yari bisa zargin satar wayar wutar lantarki a Kano.Masarautar Gumel ta haramta ɗaukar hotuna da Bidiyo a fadar sarki ba tare da izini ba.El-rufa'i ya musanta zargin sauraron wayar Nuhu Ribadu a Kotu.Ma'aikacin Kanawa Radio Kano, Umar Tijjani Sabi'u (No Time) ya rasu.Kwankwaso ya musanta aike Gwamna Abba Yusuf zuwa wajen Tinubu don tattaunawa kan komawarsu APC.Hukumar Shari'a ta sulhunta ƴan siyasar da ke jifan juna da munanan kalamai a Kano.Kotu ta aike da Abubakar Uran gidan yari bisa zargin satar wayar wutar lantarki a Kano.Masarautar Gumel ta haramta ɗaukar hotuna da Bidiyo a fadar sarki ba tare da izini ba.El-rufa'i ya musanta zargin sauraron wayar Nuhu Ribadu a Kotu.Ma'aikacin Kanawa Radio Kano, Umar Tijjani Sabi'u (No Time) ya rasu.Kwankwaso ya musanta aike Gwamna Abba Yusuf zuwa wajen Tinubu don tattaunawa kan komawarsu APC.Hukumar Shari'a ta sulhunta ƴan siyasar da ke jifan juna da munanan kalamai a Kano.
← Labarai
Labarai

Ma'aikacin Kanawa Radio Kano, Umar Tijjani Sabi'u (No Time) ya rasu.

Allah Ya yi wa shugaban sashen shirye-shirye na Gidan Radio Kanawa Umar Tijjani Sabi'u ( No Time) rasuwa.

Marigayin, na daga cikin fitattun ma’aikatan gidan rediyon Express da Kanawa, Kano, wanda ya yi fice wajen faɗakarwa, ilimantarwa da kuma nishaɗantar da al'umma a yayin gudanar da aikin sa.

Umar Tijjani, wanda tsohon Shugaban Ƙungiyar Masu Gabatar da Shirye-shirye ta Jihar Kano (Kano On-Air Personalities Forum) ne, ya rasu ne a yau Laraba, 25 ga watan Nuwambar 2026.

Wannan na cikin sanarwar ta’aziyya da Shugaban Ƙungiyar Masu Gabatar da Shirye-shirye ta Kano, Rabi’u Ahmad Ƙofar Mazugal, ya fitar, za a gudanar da sallar jana’izar marigayin da misalin ƙarfe 2:00 na rana a gidan Alhaji Tijjani Sabi’u, da ke unguwar Gwammaja, Layin Sakatariyar Ƙaramar Hukumar Dala.

Ƙungiyar ta yi addu’ar Allah ya jiƙansa da rahama, ya gafarta masa kurakuransa, ya haskaka kabarinsa, tare da sanya Aljannatul Firdausi ta zama makomarsa.

Ƴan Jarida da sauran al'umma da ma ne ke ci gaba da bayyana alhinin su dangane da rayuwar Marigayin, suna addu'ar Allah ya jiƙansa da gafara.

Dala FM Kano 88.5 FM
Dala FM Kano 88.5 FM · Kai tsaye
Live