Labarai
Hukumar Shari'a ta sulhunta ƴan siyasar da ke jifan juna da munanan kalamai a Kano.

Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ta yi zama na biyu tare da wasu ƴan siyasa (Sojojin Baka) domin daidaita saɓanin da ke tsakanin wasu daga cikin su har ta kai suna cin mutuncin juna da yi wa junan su ƙazafi wanda hakan ya saɓawa shari'ar Allah S.W.T.
Shugaban Hukumar shari'ar a Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya jagoranci zaman karo na biyu a ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba, 2026.
A ƴan kwanakin bayan nan ne dai aka hango ƴan siyasar na cin mutuncin junan su a shafukan sada zumunta na zamani, da kuma jin su a wasu kafafen yaɗa labarai, al'amarin da ke kawo tasgaro ga tarbiyya.
Da yake ƙarin bayani a kan zaman, Kwamishina na biyu a Hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, ya ce a yayin zaman an sulhunta tsakanin Alhajiji Nagoda da amininsa Shamsu Kura, sai kuma Gamboliya Ja'en da Sunusi Kata Madobi, bayan da suka daɗe suna jifan junansu da maganganun da basu dace ba.
A yayin sulhun nasu, ƴan siyasar sun yafewa junan su tare da alƙawarin ba za a sake jin irin ƙazantattun maganganun da aka rinƙa jin su suna furta wa junan su ba a baya.
Sheikh Ali Ɗanabba ya kuma yi addu'ar Allah ya ƙara haɗa zukatan su ya yafe musu, ya sadar da su da rahamar sa.
Shima a yayin zaman, Kwamishina na ɗaya a hukumar shari'ar, Gwani Ɗahir Hadi Yakasai, ya buƙaci ƴan siyasar da su ƙara sanya tsoron Allah a zukatan su, tare da ƙara mutunta junan su.
A makon da ya gabata ne dai Hukumar Shari'ar ta zauna da wasu daga cikin ƴan siyasar da suke jifan juna da munanan kalamai a shafukan sada zumunta da kafafen yaɗa labarai, biyo bayan fuskantar samun saɓani a tsakanin su.


