Dala FM
Muryar Jama'a
Yanzu-yanzu
Hakimai, dagatai, ku zauna da shugabannin Fulani da manoma don ƙarfafa zaman lafiya a Ungogo - Sarkin KanoAn sake tsintar wani Jariri sabuwar haihuwa a Ƙofar Na'isa da ke Kano.Shugabannin APC ku yafe wa juna tare da haɗa kai gabanin zaben 2027 - TinubuAn tsinci ƴan tagwayen jarirai sabuwar haihuwa a yankin Ɗorayi da ke Kano.Saboda a raba ni da mata ta har gida aka zo aka kwashe kayan ta, aka yi garkuwa da ita - Gwamnan Kano.Saboda a raba ni da mata ta har gida aka zo aka kwashe kayan ta, aka yi garkuwa da ita - Gwamnan KanoHakimai, dagatai, ku zauna da shugabannin Fulani da manoma don ƙarfafa zaman lafiya a Ungogo - Sarkin KanoAn sake tsintar wani Jariri sabuwar haihuwa a Ƙofar Na'isa da ke Kano.Shugabannin APC ku yafe wa juna tare da haɗa kai gabanin zaben 2027 - TinubuAn tsinci ƴan tagwayen jarirai sabuwar haihuwa a yankin Ɗorayi da ke Kano.Saboda a raba ni da mata ta har gida aka zo aka kwashe kayan ta, aka yi garkuwa da ita - Gwamnan Kano.Saboda a raba ni da mata ta har gida aka zo aka kwashe kayan ta, aka yi garkuwa da ita - Gwamnan Kano
← Labarai
Labarai

Abba Hikima ya yi fatali da kyautar filin da gwamnatin jihar Kaduna ta ba shi.

Jagoran ƙungiyar Tinubu Must Go (TMG), Abba Hikima, ya yi fatali da filin da gwamnatin jihar Kaduna ta ba shi, bisa zargin cewa ana gallaza wa mambobin ƙungiyar a jihar.

Hikima, wanda lauya ne, ya ce amincewa da karɓar filin na iya kawo shakku kan ’yancin kansa tare da rage masa ƙarfin sukar gwamnati da kuma kare muradun mambobin ƙungiyar.

Ya bayyana hakan ne cikin wata wasiƙa mai kwanan watan 23 ga Nuwamba, 2026, wadda ya aikewa Gwamnan Kaduna tare da isar da ita fadar gwamnatin jihar a ranar.

A cikin wasiƙar mai taken ƙin amincewa da filin mai lamba 484387, Hikima ya ce ya samu sanarwar bayar da filin ne a ranar 19 ga Nuwamba, duk da cewa an fitar da tayin tun ranar 22 ga Oktoba, 2026.

Ya gode wa gwamnan bisa tayin, amma ya ce bai taɓa neman filin ba, kuma yanayin da aka yi tayin a cikinsa ya sanya shi rashin jin daɗin karɓarsa.

Hikima ya zargi hukumomin jihar da gallaza wa mambobin TMG ta hanyar kama su, tsoratar da su da kuma hana su gudanar da wasu ayyukansu.

Ya kuma koka kan yadda mambobin ƙungiyar ke fuskantar matsaloli wajen buga rigunan kamfen masu tambarin ƙungiyar a Kaduna, duk da cewa a cewarsa, ba sa aikata wani abu da ya saɓa wa doka.

Ya ce ba sa fuskantar irin waɗannan matsaloli a wasu jihohin ƙasar, inda mambobin ƙungiyar ke samun damar buga kayan kamfen ɗinsu ba tare da tangarɗa ba.

A kalamansa, “A irin wannan yanayi, karɓar wani fili na kashin kai daga mai girma gwamna na iya kawo cikas ga ’yancin kaina, tare da rage ƙarfin da nake da shi na fuskantar waɗannan matsaloli cikin cikakken ’yanci da ƙarfin hali da ake buƙata wajen jagorantar al'ummata.”

Saboda haka, Hikima ya sanar da gwamnan cewa ya yi watsi da tayin filin a hukumance, kamar yadda kafar Daily Nigerian ta ruwaito.

Ƙungiyar Tinubu Must Go dai wata ƙungiyar matsin lamba ce ta siyasa da ke adawa da gwamnatin Shugaba Bola Tinubu da kuma yiwuwar sake tsayawa takararsa a zaɓen shugaban ƙasa na 2027.

Dala FM Kano 88.5 FM
Dala FM Kano 88.5 FM · Kai tsaye
Live