Labarai
Kotu ta umarci hukumar KCPC ta lalata wani Taki na ruwa na miliyoyin kuɗaɗe da ta kama a Kano.

Hukumar kare Hakkin Mai saye ta jihar Kano, ta Sami nasara a kotu bayan da ta bada umarnin lalata wani Taki na ruwa da ta kama na miliyoyin kuɗaɗe da ake kokarin Canja masa mazubi domin shigar da shi kasuwa.
Dala FM Kano ta ruwaito cewa, wannan na cikin sanarwar da Daraktan Wayar da Kai na Hukumar KCPC, Jamilu Mustapha Yakasai, ya fitar a ranar Juma'a 20 ga watan Nuwamba, 2026.
Sanarwar ta ce hakan na daga cikin kokarin Hukumar na daƙile yaɗuwar gurɓatattun kayayyaki da waɗanda wa'adin su ya ƙare a kasuwannin jihar Kano.
Da yake jawabin a kan lamarin, Sakataren Zartarwa na Hukumar KCPC, Dr. Ibarahim Garba Muhammad ya ce Hukumar nayin duk mai yiyuwa wajen ganin al'umma ba su faɗa wani yanayi da ka iya jefa lafiyar su cikin wani yanayi mara daɗi ba.
Ya kara da cewa ko a makwannin da su gabata, Hukumar ta sami nasarar kama wata madara da wa'adin ta ya ƙare da ake kokarin canja mata mazubi.
Dr. Ibrahim ya kuma jaddada buƙatar sa ga al'umma kan su cigaba da bawa Hukumar hadin kai, yana mai cewa hakan zai taimaka matuka wajen yaki da irin waɗannan ɓata gari


