Labarai
Zan mayar da hankali wajen ƙwato haƙƙin waɗanda aka cuta a Kano - Sabon Daraktan ƙungiyar haƙƙin ɗan adam

Sabon Daraktan Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Global Community for Human Right Network, na jihar Kano, Kwamared Muhammad AA King, ya ce zai mayar da hankali kan ƙwato haƙƙin mutane ba sani babu sabo.
Kwamared Muhammad AA King, ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan da kwamitin samar da shugabanci na ƙungiyar ta Global Community for Human Right Network, ya miƙa masa takardar kama aiki a matsayin Daraktan Ƙungiyar a matakin jihar Kano, a ranar Alhamis 19 ga watan Nuwamba, 2026.
Kwamared Muhammad AA King, ya kuma ƙara da cewa, zai mayar da hankali wajen bibiyar haƙƙoƙin mutanen da aka cuta, kama daga wajen jami'an tsaro har zuwa kotuna, da kuma sulhunta ma'aurata da dai sauransu.
Da yake nasa jawabin, Shugaban Kwamitin samar da shugabanci da tantance waɗanda za a naɗa a muƙamai daban-daban a ƙungiyar, kuma Babban Daraktan Ƙungiyar kare haƙƙin ɗan adam ta Sustainable Growth iniatives for Human Right and charity development, Kwamared Abubakar Musa Abdullahi, ya buƙaci sabbin shugabannin da su jajirce wajen samar da ci gaba ga al'umma.
Ya kuma buƙaci sabbin shugabannin da su gudanar da aiki bisa gaskiya da riƙon amana, tare da jajircewa.
Yahaya G Alhassan shi ne sabon mai magana da yawun ƙungiyar ta Global Community for Human Right Network, na jihar Kano, ya ce za su yi bakin ƙoƙarin su wajen sauke nauyin da aka ɗora musu.
An naɗa Hajiya Hauwa Adam a matsayin Mataimakiyar Daraktar ƙungiyar, da Alhaji Sammani Shawus a matsayin mashawarcin ƙungiyar a kan harkar Shari'a, sai Mallam Sunusi Ahmad Soron dinki, a matsayin Shugaban Kwamitin amintattu na ƙungiyar da dai sauran shugabanni.


