Shari'a
Kotu ta aike da Abubakar Uran gidan yari bisa zargin satar wayar wutar lantarki a Kano.

Rundunar ƴan Sanda ta gurfanar da Abubakar Alhaji Sha'aibu, a gaban Kotun shari'ar musulunci da ke Jogana, ƙarƙashin mai Shari'a Kamalu Haruna Durumin iya.
Tunda fari, Dagacin garin Uran Alhaji Isyaku, ne ya yi ƙorafi cewa, ya je garin Uran yana yanke wayar wuta ta haya tanshin lokacin bincike ya sheda Wasu mutane biyu.
A yayin zaman kotun na ranar Laraba 25 ga Nuwamba, 2026, mai gabatar da ƙara Inspector Murtala Kabara ya karanta masa ƙunshin tuhumar inda ya amsa.
Mai gabatar da ƙara ya nemi a basu wata ranar kasancewar har yanzu yansanda suna menan mutane biyu da ya ambaci sunansu cewa sune suke siyan wanan kaya.
Wakilinmu Yusif Nadabo Isma'il ya ruwaito cewa, kotun ta aike da shi zuwa gidan gyaran gali har zuwa ranar 30 ga wanan wata na Nuwamba domin cigaba da sauraron shari'ar.


