Shari'a
Kotu ta yanke wa Bamfasi hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari a Kano.

Babbar Kotun Jiha da ke Miller Road, Kano, ƙarƙashin jagorancin Mai Shari’a Maryam Sabo, ta yanke wa Aminu Sulaiman, wanda aka fi sani da Bamfasi, hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari bayan samunsa da laifin haɗin baki da garkuwa da wani yaro.
Gwamnatin Kano ce ta gurfanar da Bamfasi tare da Abdurrashid Ishak, wanda ya rasu a gidan gyaran hali, bisa tuhume-tuhumen haɗin baki wajen aikata laifi, garkuwa da mutane da kuma kisan kai. Lauyar gwamnati, Barista S. M. Ibrahim, ta gabatar da shaidu biyu a lokacin shari’ar.
A zaman kotun na ranar Alhamis 26 ga Nuwamba, 2026, Mai Shari’a Maryam Sabo, ta yanke masa hukuncin shekaru shida kan laifin haɗin baki da kuma shekaru huɗu kan garkuwa da mutane. Sai dai kotun ta ce zai shafe shekaru 14 a gidan yari, tare da yin aikin shekara biyu a cikin gidan gyaran hali. Kotun ba ta same shi da laifin kisan kai ba saboda rashin isassun hujjoji.
Lamarin ya faru ne a unguwar Kwanar Hudu, inda aka yi garkuwa da Muhammad Abdulaziz tare da neman kuɗin fansa na Naira 150,000, kafin daga bisani aka gano gawarsa a wani ƙauye da ke ƙaramar hukumar Minjibir.


