Labarai
Hukumar Shari'a ta Kano, ta sulhunta ƴan siyasa Gamboliya Ja'en da Ali Gyara Hausawa, bayan shekaru uku ba sa magana.

Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ta sulhunta ƴan siyasar nan Gamboliya Ja'en da Ali Gyara Hausawa, bayan da suka kai kusan shekaru uku basa magana da junan su bisa wani saɓani da suka samu a baya.
Wannan na zuwa ne biyo bayan wani zama da hukumar ta gudanar tare da wasu daga cikin ƴan siyasa domin faɗakar da su kan illar cin mutuncin juna wasun su suke yi a shafukan sada zumunta na zamani.
Shugaban Hukumar Shari'ar ta jihar Kano, Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya jagoranci zaman ranar Alhamis 19 ga watan Nuwamba, 2026, a ofishin sa da ke Kano.
Ƴan siyasar da suka halarci zaman sun haɗar da Alhajiji Nagoda, da Ali Gyara Hausawa, Ibrahim Soja Kantin Kwari, Gamboliya Ja'en, da Nura Bakwankwashe, sai wakilcin Abdulmajid Ɗan Bilki Kwamanda, da Da sauransu.
Wani abun gwanin ban sha'awa, a yayin zaman ne Gamboliya Ja'en ya tono tsohuwar gabar da ke tsakanin sa da Ali Gyara Hausawa, bayan da suka kai kusan shekaru uku ba sa magana, inda nan take hukumar ta sulhunta su.
Ƴan siyasar sun ce sun samu wani saɓani ne a baya a tsakanin su lamarin da ya yi munin gaske har ta kai ga sun daina magana a tsakanin su kusan shekaru uku.
Mutanen biyu dai sun yafewa junan su tare da gaisawa da juna a yayin zaman, cikin farin ciki da kuma barkwanci.
A yayin zaman da aka gudanar, Kwamishina na ɗaya a hukumar Shari'a ta jihar Kano, Gwani Ɗahir Hadi Yakasai, da na biyu Sheikh Ali Ɗanabba, sun faɗakar da ƴan siyasar kan su ji tsoron Allah, su daina cin mutuncin junan su.
Dukkanin ƴan siyasar da suka halarci zaman sun yi alƙawarin ba za a sake samun su da cin mutuncin kowa ba a siyasa, za su rinƙa tsaftace kalaman su yayin magana a kan siyasa.


