Dala FM
Muryar Jama'a
Yanzu-yanzu
Kwankwaso ya musanta aike Gwamna Abba Yusuf zuwa wajen Tinubu don tattaunawa kan komawarsu APC.Hukumar Shari'a ta sulhunta ƴan siyasar da ke jifan juna da munanan kalamai a Kano.Ana zargin ɓata gari sun sace wayoyin wutar lantarki a falwayoyi 11 a Chiromawa da ke Kano.Hakimai, dagatai, ku zauna da shugabannin Fulani da manoma don ƙarfafa zaman lafiya a Ungogo - Sarkin KanoAn sake tsintar wani Jariri sabuwar haihuwa a Ƙofar Na'isa da ke Kano.Shugabannin APC ku yafe wa juna tare da haɗa kai gabanin zaben 2027 - TinubuKwankwaso ya musanta aike Gwamna Abba Yusuf zuwa wajen Tinubu don tattaunawa kan komawarsu APC.Hukumar Shari'a ta sulhunta ƴan siyasar da ke jifan juna da munanan kalamai a Kano.Ana zargin ɓata gari sun sace wayoyin wutar lantarki a falwayoyi 11 a Chiromawa da ke Kano.Hakimai, dagatai, ku zauna da shugabannin Fulani da manoma don ƙarfafa zaman lafiya a Ungogo - Sarkin KanoAn sake tsintar wani Jariri sabuwar haihuwa a Ƙofar Na'isa da ke Kano.Shugabannin APC ku yafe wa juna tare da haɗa kai gabanin zaben 2027 - Tinubu
← Labarai
Labarai

Ana zargin ɓata gari sun sace wayoyin wutar lantarki a falwayoyi 11 a Chiromawa da ke Kano.

Ana zargin wasu ɓata gari da sace wayoyin lantarki daga falwayoyi 11 tsakanin Garin Tsaure na Mazabar Fankurun da Garin Chiromawa, a Ƙaramar Hukumar Garun Mallam ta Jihar Kano.

Wani mazaunin yankin Musa Abbas Garun-mallam ya shaidawa Arewa update cewa, wayoyin da ake zargin an sace na cikin kayayyakin samar da wutar lantarki da al’ummomin yankin ke amfani da su.

Haka kuma, ya buƙaci hukumomin tsaro su gudanar da bincike domin gano waɗanda ake zargin sun aikata satar, tare da ɗaukar matakan da suka dace.

Wannan al'amari dai ya tayar da hankulan al'ummar yankin, la'akari da yadda lamarin ya yi munin gaske.

Dala FM Kano 88.5 FM
Dala FM Kano 88.5 FM · Kai tsaye
Live