Masarauta
Masarautar Gumel ta haramta ɗaukar hotuna da Bidiyo a fadar sarki ba tare da izini ba.

Majalisar Masarautar Gumel da ke Jihar Jigawa ta haramta ɗaukar hotuna da bidiyo a cikin fadar sarki, tare da wallafa bayanan da suka shafi masarautar ba tare da izini ba.
Masarautar ta bayyana cewa duk wanda ke son ɗaukar hotuna ko bidiyo, ko kuma ya wallafa wani bayani da ya shafi fadar, dole ne ya fara samun izini daga mahukuntan masarautar.
Haka kuma, majalisar ta yi gargaɗin cewa za ta ɗauki matakin shari’a kan duk wanda ya karya wannan doka.
An ce matakin na da nufin sanya ido kan yadda ake ɗaukar hotuna da bidiyo da kuma yadda ake yaɗa bayanan da suka shafi masarautar.
Masarautar ta jaddada cewa wajibi ne a bi ƙa’idojin da aka gindaya domin kauce wa karya dokar.


