Dala FM
Muryar Jama'a
Yanzu-yanzu
Kotu ta aike da Abubakar Uran gidan yari bisa zargin satar wayar wutar lantarki a Kano.Masarautar Gumel ta haramta ɗaukar hotuna da Bidiyo a fadar sarki ba tare da izini ba.El-rufa'i ya musanta zargin sauraron wayar Nuhu Ribadu a Kotu.Ma'aikacin Kanawa Radio Kano, Umar Tijjani Sabi'u (No Time) ya rasu.Kwankwaso ya musanta aike Gwamna Abba Yusuf zuwa wajen Tinubu don tattaunawa kan komawarsu APC.Hukumar Shari'a ta sulhunta ƴan siyasar da ke jifan juna da munanan kalamai a Kano.Kotu ta aike da Abubakar Uran gidan yari bisa zargin satar wayar wutar lantarki a Kano.Masarautar Gumel ta haramta ɗaukar hotuna da Bidiyo a fadar sarki ba tare da izini ba.El-rufa'i ya musanta zargin sauraron wayar Nuhu Ribadu a Kotu.Ma'aikacin Kanawa Radio Kano, Umar Tijjani Sabi'u (No Time) ya rasu.Kwankwaso ya musanta aike Gwamna Abba Yusuf zuwa wajen Tinubu don tattaunawa kan komawarsu APC.Hukumar Shari'a ta sulhunta ƴan siyasar da ke jifan juna da munanan kalamai a Kano.
← Labarai
Masarauta

Hakimai, dagatai, ku zauna da shugabannin Fulani da manoma don ƙarfafa zaman lafiya a Ungogo - Sarkin Kano

Mai Martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimai da dagatai da masu unguwanni, da su cigaba da wayar dakan Fulani makiyaya da manoma mahimmancin zaman lafiya a tsakaninsu.

Sarkin ya bayyana hakan ne ta bakin muƙaddashin babban ɗan majalisar sarki, kuma Magajin garin Kano Alhaji Nasiru Inuwa, a yayin zaman majalisar masarautar Kano na ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba, 2026.

Sarkin ya ce kasancewar zaman lafiya abu ne mai mutuƙar mahimmanci a don haka ya umarci dagatai da masu unguwanni su rinƙa saurin sanar da hakimansu duk wani abu da suka gani zai kawo rashin zaman lafiya a yankunansu ba sai abin ya faru ba.

Haka kuma, Sarkin ya buƙaci hakimai da dagatai da kuma masu unguwanni, da su zauna da shugabannin fulani da ma na manoma kan yadda za'a rinƙa samun zaman lafiya a tsakaninsu.

Wakilinmu Shamsu Da'u Abdullahi ya ruwaito cewa, umarnin sarkin na zuwa ne a dai dai lokacin da aka gabatar da wata takarda kan yadda ake zargin wasu fulani a ƙaramar hukumar Ungogo, inda aka samu rikici tsakanin manoma da makiyaya a unguwar rijiyar zaki da kuma Unguwar rimin zaka a tsakanin su da manoma.

Dala FM Kano 88.5 FM
Dala FM Kano 88.5 FM · Kai tsaye
Live