Labarai
Gwamnatin Kano ta bai wa kwamitin binciken zargin cin hanci a makarantun lafiya wa'adin mako ɗaya.

Gwamnatin Jihar Kano ta bayar da wa'adin mako guda ga kwamitin da ta kaddamar kan zarge-zargen cin hanci da rashawa da ake yi wa Shugaban Kwalejin Koyon Aikin Jinya ta Kano (School of Nursing Kano) da wasu manyan jami’an gudanarwar kwalejin.
Kwamishinan Yaɗa Labarai da Harkokin Cikin Gida na jihar, Alhaji Sunusi Bature Dawakin Tofa, ne Ya bayyana hakan yayin da yake zantawa da manema labarai jim kaɗan bayan kammala zaman farko na kwamitin.
Ya ce za su gudanar da cikakken bincike domin gano gaskiyar zarge-zargen da ake yi, inda ya bayyana cewa gwamnatin jihar ta ba su wa’adin mako guda domin kammala binciken tare da gabatar da rahotonsu.
Sunusi Bature Dawakin Tofa ya ƙara da cewa, kwamitin zai gabatar da shawarwarin da suka dace ga Gwamna Abba Kabir Yusuf domin ɗaukar matakin da ya dace bisa sakamakon binciken.


