Dala FM
Muryar Jama'a
Yanzu-yanzu
Rundunar Kossap ta kama Aliyu Ashiru kan zargin sayar da ƙwayoyi da zagin Muhyi Magaji Rimin a Kano.Hukumar Shari'a ta Kano, ta sulhunta ƴan siyasa Gamboliya Ja'en da Ali Gyara Hausawa, bayan shekaru uku ba sa magana.Gwamnatin Kano ta bai wa kwamitin binciken zargin cin hanci a makarantun lafiya wa'adin mako ɗaya.Kotu ta umarci hukumar KCPC ta lalata wani Taki na ruwa na miliyoyin kuɗaɗe da ta kama a Kano.Kotu ta yi watsi da bukatar Atiku na neman gyara ƙarar da ya shigar kan Shugaba Tinubu da APC.Zan mayar da hankali wajen ƙwato haƙƙin waɗanda aka cuta a Kano - Sabon Daraktan GCHRNRundunar Kossap ta kama Aliyu Ashiru kan zargin sayar da ƙwayoyi da zagin Muhyi Magaji Rimin a Kano.Hukumar Shari'a ta Kano, ta sulhunta ƴan siyasa Gamboliya Ja'en da Ali Gyara Hausawa, bayan shekaru uku ba sa magana.Gwamnatin Kano ta bai wa kwamitin binciken zargin cin hanci a makarantun lafiya wa'adin mako ɗaya.Kotu ta umarci hukumar KCPC ta lalata wani Taki na ruwa na miliyoyin kuɗaɗe da ta kama a Kano.Kotu ta yi watsi da bukatar Atiku na neman gyara ƙarar da ya shigar kan Shugaba Tinubu da APC.Zan mayar da hankali wajen ƙwato haƙƙin waɗanda aka cuta a Kano - Sabon Daraktan GCHRN
← Labarai
Tsaro

Rundunar Kossap ta kama Aliyu Ashiru kan zargin sayar da ƙwayoyi da zagin Muhyi Magaji Rimin a Kano.

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da hana sha da dillancin kayan maye, ta Anti-illicit drugs and Phone Snaching force a Kano, ta cafke matashi Aliyu Ashiru bisa zargin sa da sayar da ƙwayoyi da kuma zagin Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, a shafukan sada zumunta.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, Babban Kwamandan rundunar da akafi sani da Kossap a Kano, Nura Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana hakan yayin zantawar sa da Dala FM Kano, a ranar Juma'a 20 ga watan Nuwamba, 2026.

Ya ce tun da farko, jami'an su sun kai sumame ne wata mafakar masu sayar da miyagun ƙwayoyi da ke unguwar Nalado Tukuntawa a ƙaramar hukumar Birnin Kano (Kano Municipal) sai dai a lokacin ya gudu ya bar ƙwayoyin da yake sayar wa guda 435.

A cewar sa, daga bisani ne aka hango matashi Aliyu Ashiru ya yi wani bidiyo da ya ɗora a shafukan sada zumunta na zamani, inda ya rinƙa zagin shugaban kwamitin karta-kwana da ke yaƙi da ta'ammali da miyagun ƙwayoyi da faɗan daba na jihar Kano, Barista Muhyi Magaji Rimin Gado.

Nura Sharaɗa ya ce bayan hakan ne ya tura jami'an sa lungu da saƙo har suka kamo Aliyu Ashiru, kuma tuni ya bada umarni aka miƙa matashin zuwa ga Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, don ɗaukar mataki na gaba a kan sa.

Da yake jawabi, matashi Aliyu Ashiru, ya tabbatar da cewa miyagun ƙwayoyin da aka kama guda 435, nasa ne, kuma ya gudu ya bar su ne saboda kada a kama shi, amma ya yi nadama.

Matashin ya kuma roƙi Barista Muhyi Magaji Rimin Gado, da ya yi haƙuri kan zagin da ya yi masa, yana mai cewa sharrin shaiɗan ne ya sa shi aikata hakan, amma ba zai ƙara ba.

Daga bisani Babban Kwamandan rundunar tsaro ta Anti-illicit drugs and Phone Snaching force a Kano, Nura Salisu Sharaɗa, ya gargaɗi dukkan masu aikata irin wannan laifi da su daina, yana mai cewa ba za su saurara wa duk wanda suka kama da aikata laifi ba.

Dala FM Kano 88.5 FM
Dala FM Kano 88.5 FM · Kai tsaye
Live