Dala FM
Muryar Jama'a
Yanzu-yanzu
Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa ta buƙaci matasa su tashi tsaye wajen samar wa yankunan su ci gaba.Gwamnatin Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na yau Asabar.Gwamnatin Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na yau Asabar a jihar.Hukumar Shari'a ta jagoranci buɗe sabon masallacin juma'a a garin Tiga dake Kano.Kwankwaso ya zargi Gwamna Abba da amfani da hukumomin yaƙi cin hanci da rashawa wajen yaƙar sa a siyasance.Hukumar Shari'a ta buƙaci gudunmawar masu jaridun internet don daƙile kalaman cin mutunci a Kano.Ƙungiyar Gamayyar Matasan Arewa ta buƙaci matasa su tashi tsaye wajen samar wa yankunan su ci gaba.Gwamnatin Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na yau Asabar.Gwamnatin Kano ta dakatar da aikin tsaftar muhalli na yau Asabar a jihar.Hukumar Shari'a ta jagoranci buɗe sabon masallacin juma'a a garin Tiga dake Kano.Kwankwaso ya zargi Gwamna Abba da amfani da hukumomin yaƙi cin hanci da rashawa wajen yaƙar sa a siyasance.Hukumar Shari'a ta buƙaci gudunmawar masu jaridun internet don daƙile kalaman cin mutunci a Kano.
← Labarai
Addini

Hukumar Shari'a ta jagoranci buɗe sabon masallacin juma'a a garin Tiga dake Kano.

Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ƙarƙashin jagorancin Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ta jagoranci buɗe sabon masallacin juma'a mai suna Al-Imam albany a garin Tiga da ke ƙaramar hukumar Bebeji ta jihar Kano.

Kwamishina na biyu a hukumar, Sheikh Ali Ɗanabba, ne ya jagoranci buɗe sabon masallacin a ranar Juma'a 27 ga watan Nuwamba, 2026.

A yayin da yake gabatar da huduba a sabon masallacin, Sheikh Ali Ɗanabba ya buƙaci al'umma da su ji tsoron Allah, tare da rinƙa sallar juma'a cikin tsafta da kuma gujewa surutu a masallacin domin rabauta da rahamar Allah S.W.T.

Malamin ya kuma yi wa limamai da shugabannin kwamitin kula da masallacin nasiha, da su ji tsoron Allah maɗaukakin Sarki, a yayin tafikar da ayyuka a masallacin.

Dala FM Kano ta ruwaito cewa, an naɗa Mallam Muhammad Auwal Sale a matsayin limamin masallacin na ɗaya, yayin da aka naɗa Malam Sulaiman Aminu, a matsayin limami na biyu, da kuma naɗa ladanai da sauran shugabanni a Masallacin.

Al'umma da dama ne dai suka samu damar halartar buɗe sabon masallacin juma'ar ciki har da jami'an tsaron Ƴan Sanda, da na Hisbah, da wakilcin dagacin garin Gwarmai, da wakilci daga ɓangaren malamai, ƴan siyasa, masu riƙe da sarautun gargajiya da dai sauransu.

Dala FM Kano 88.5 FM
Dala FM Kano 88.5 FM · Kai tsaye
Live