Dala FM
Muryar Jama'a
Yanzu-yanzu
Kotu ta yanke wa Bamfasi hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari a Kano.Ba za a saka sunayen jam’iyyun siyasa a takardun zaɓen gwaji ba - INECRundunar Anti-Phone Snaching ta kama Yusuf Abdullahi da Ƙwayoyi 350, da tabar wiwi kofi 10 a Kano.Kotu ta aike da Abubakar Uran gidan yari bisa zargin satar wayar wutar lantarki a Kano.Masarautar Gumel ta haramta ɗaukar hotuna da Bidiyo a fadar sarki ba tare da izini ba.El-rufa'i ya musanta zargin sauraron wayar Nuhu Ribadu a Kotu.Kotu ta yanke wa Bamfasi hukuncin ɗaurin shekaru 14 a gidan yari a Kano.Ba za a saka sunayen jam’iyyun siyasa a takardun zaɓen gwaji ba - INECRundunar Anti-Phone Snaching ta kama Yusuf Abdullahi da Ƙwayoyi 350, da tabar wiwi kofi 10 a Kano.Kotu ta aike da Abubakar Uran gidan yari bisa zargin satar wayar wutar lantarki a Kano.Masarautar Gumel ta haramta ɗaukar hotuna da Bidiyo a fadar sarki ba tare da izini ba.El-rufa'i ya musanta zargin sauraron wayar Nuhu Ribadu a Kotu.
← Labarai
Tsaro

Rundunar Anti-Phone Snaching ta kama Yusuf Abdullahi da Ƙwayoyi 350, da tabar wiwi kofi 10 a Kano.

Rundunar tsaro da ke yaƙi da faɗan daba da ƙwacen waya da kuma daƙile sha da dillancin kayan maye ta Anti-illicit drugs/Phone Snaching force ta jihar Kano, ta kama matashi Yusif Abdullahi, mai shekaru 21, bisa zargin sa da sayar da Ƙwayoyi da Tabar wiwi a yankin Fagge.

Kwamandan rundunar a Kano, CMD Nura Salisu Sharaɗa, ne ya bayyana wa Dala FM Kano, kama matashin a ranar Alhamis 26 ga watan Nuwamba, 2026.

Ya ce matashin mai suna Yusuf Abdullahi, an kama shi ne ɗauke da tarin Ƙwayoyin Exsol, guda 350, da kuma kofin tabar wiwi guda goma, inda aka yi zargin yana sayar wa a yankin ƙaramar hukumar Fagge da ke Kano.

A cewar Nura Sharaɗa, bayan da suka samu bayanan sirri ne kan yadda wasu matasa suke sayar da miyagun ƙwayoyi da tabar wiwi, ya tura jami'an sa na 'Damisa Ƙi Sabo' inda suka tarwatsa masu sayar da kayan mayen tare da kama matashi Yusif Abdullahi.

Ya ce yanzu haka suna gudanar da bincike a kan matashin kuma da zarar sun kammala za su miƙa shi inda ya dace domin ɗaukar mataki na gaba a kan sa.

Da yake yi wa Dala FM ƙarin bayani, Matashin Yusuf ya ce, rashin taimaka masa da masu gidan sa ƴan siyasa suka yi kan lalurar da take damun sa ne ya jefa shi cikin dillancin kayan maye, domin ya rinƙa samun ɗan na abinci tare da taimaka wa mahaifiyar sa da kuma ƙanwar sa.

Sai dai matashin ya bayyana takaicin sa kan yadda masu gidan sa, wato ƴan siyasar da suka daɗe suna yi wa bangar siyasa suka gaza taimaka masa, kan yadda za a yi masa tiyata bisa kwailayewar wani ɓangare na jikin sa, a don haka yake nadama a kan irin gudunmawar da ya basu.

Daga bisani Nura Sharaɗa, ya kuma gargaɗi dukkan ɓata garin da suke addabar jama'a da aikata laifuka irin daban-daban da su daina, domin duk wanda ya faɗa komar su da aikata laifin ba za su saurara masa ba.

Dala FM Kano 88.5 FM
Dala FM Kano 88.5 FM · Kai tsaye
Live