Siyasa
Shugabannin APC ku yafe wa juna tare da haɗa kai gabanin zaben 2027 - Tinubu

Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya bukaci shugabanni da jiga-jigan jam’iyyar APC da su sasanta tsakaninsu tare da yafewa juna duk wani sabani da ke tsakaninsu domin karfafa hadin kai a jam’iyyar gabanin zaben shekarar 2027.
Tinubu ya bayyana hakan ne yayin wani taron addu’a na musamman da aka shirya masa a birnin Legas.
Shugaban ya ce ya kamata shugabannin jam’iyyar su ajiye bambance-bambancen da ke tsakaninsu, su kuma mayar da hankali wajen hada kai domin tunkarar zaben 2027.
Ya kuma bukaci wasu daga cikin manyan jami’an jam’iyyar da su taimaka wajen sasanta rikice-rikicen da ke tsakanin shugabanni a wasu jihohin kasar.
Tinubu ya bukaci mai ba shi shawara kan harkokin siyasa, Ibrahim Kabiru Masari, da ya taimaka wajen sasanta sabanin da ke tsakaninsa da Gwamnan Jihar Katsina, Dikko Umar Radda.
Haka kuma, ya bukaci tsohon Ministan Tsaro, Abubakar Badaru, da ya taka rawa wajen samar da zaman lafiya da fahimtar juna tsakanin shugabannin jam’iyyar ta APC.
A yayin jawabin nasa, shugaban ya jaddada cewa yafiya da hadin kai na da matukar muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiyar jam’iyyar da kuma shirye-shiryenta na babban zaben 2027.
Kafar yaɗa labarai ta BBC ta ruwaito cewa, taron ya samu halartar gwamnoni da manyan jami’an gwamnati da kuma wasu jiga-jigan jam’iyyar APC.


