Siyasa
Kwankwaso ya musanta aike Gwamna Abba Yusuf zuwa wajen Tinubu don tattaunawa kan komawarsu APC.

Mataimakin ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar NDC Sanata Rabi'u Kwankwaso, ya musanta zargin cewa ya aika Gwamnan Jihar Kano, Abba Yusuf, zuwa wajen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin tattaunawa kan shirin komawarsu jam’iyyar APC.
Sanata Kwankwaso ya musanta hakan ne a cikin wata sanarwa da kakakin ƙungiyar Kwankwasiyya, Dakta Habibu Mohammed, ya fitar a ranar Litinin, wadda aka aika wa jaridar The PUNCH.
Sanarwar ta ce: “Mun samu labarin hirar da Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya yi da BBC Hausa, inda ya yi zargin cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ne da kansa ya aika shi zuwa wajen Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu domin tattaunawa kan shirin komawarsu jam’iyyar APC.


