Masarauta
Hakimai, dagatai, ku zauna da shugabannin Fulani da manoma don ƙarfafa zaman lafiya a Ungogo - Sarkin Kano

Mai Martaba sarkin Kano Khalifa Muhammadu Sanusi na biyu, ya buƙaci dukkanin hakimai da dagatai da masu unguwanni, da su cigaba da wayar dakan Fulani makiyaya da manoma mahimmancin zaman lafiya a tsakaninsu.
Sarkin ya bayyana hakan ne ta bakin muƙaddashin babban ɗan majalisar sarki, kuma Magajin garin Kano Alhaji Nasiru Inuwa, a yayin zaman majalisar masarautar Kano na ranar Litinin 23 ga watan Nuwamba, 2026.
Sarkin ya ce kasancewar zaman lafiya abu ne mai mutuƙar mahimmanci a don haka ya umarci dagatai da masu unguwanni su rinƙa saurin sanar da hakimansu duk wani abu da suka gani zai kawo rashin zaman lafiya a yankunansu ba sai abin ya faru ba.
Haka kuma, Sarkin ya buƙaci hakimai da dagatai da kuma masu unguwanni, da su zauna da shugabannin fulani da ma na manoma kan yadda za'a rinƙa samun zaman lafiya a tsakaninsu.
Wakilinmu Shamsu Da'u Abdullahi ya ruwaito cewa, umarnin sarkin na zuwa ne a dai dai lokacin da aka gabatar da wata takarda kan yadda ake zargin wasu fulani a ƙaramar hukumar Ungogo, inda aka samu rikici tsakanin manoma da makiyaya a unguwar rijiyar zaki da kuma Unguwar rimin zaka a tsakanin su da manoma.


