Dala FM
Muryar Jama'a
Yanzu-yanzu
INEC ta musanta zargin cewa ana iya kashe na’urar BVAS ta hanyar nesa kafin a kammala zaɓe.INEC ta musanta zargin cewa ana iya kashe na’urar BVAS ta hanyar nesa kafin a kammala zaɓe.
← Labarai
Labarai

Hukumar Shari'a ta zauna da Limamai don lalubo hanyoyin gyaran tarbiyyar jama'a a Kano.

Hukumar Shari'a ta jihar Kano, ta fara zama na musamman tare da limaman masallatan Juma'a, domin miƙa buƙatar hukumar ga limaman kan su faɗakar da al'umma don gyaran tarbiyyar al'umma a jihar.

Shugaban Hukumar Shari'ar Sheikh Abbas Abubakar Daneji, ne ya jagoranci zaman a ofishin ta da ke Kano, a ranar Laraba 18 ga watan Nuwamba, 2026.

Zaman dai na zuwa ne biyo bayan yadda ake fuskantar ƙalubalen taɓarɓarewar tarbiyyar al'umma, la'akari da yadda ake samun wasu ƴan siyasa na cin mutuncin junan su a shafukan sada zumunta, da lalacewar tarbiyyar matasa, da kuma yadda wasu matasa ke ta'ammali da miyagun ƙwayoyi a jihar Kano.

Da yake jawabi, Kwamishina na biyu a Hukumar Shari'a ta jihar Kano, Sheikh Ali Ɗanabba, ya ce hukumar ta zauna da limaman ne domin ƙara lalubo hanyoyin gyaran tarbiyyar al'umma a faɗin jihar.

Sheikh Ali Ɗanabba ya kuma buƙaci shugabannin jam'iyyun siyasa da su tsawatar wa sauran ƴan siyasa, kan kaucewa cin mutuncin juna a shafukan sada zumunta da ma kafafen yaɗa labarai, domin gudun lalacewar tarbiyyar yara masu tasowa.

Sheikh Kabiru Muhammad Bature, shi ne mai magana da yawun Majalisar Limamai ta jihar Kano, kuma shugaban Limamai na ƙaramar hukumar Fagge, ya ce gayyatar da hukumar Shari'ar ta yi, ta ƙara musu ƙaimi, wajen ƙara faɗakar da al'umma domin ƙara samun gyaran tarbiyyar jama'a.

Limamai da dama ne suka samu damar halartar taron da hukumar Shari'a ta jihar Kano ta gudanar, inda aka tattauna mahimman batutuwa da dama, da za su ƙara kawo ci gaba, da kuma gyaran tarbiyyar al'umma a jihar Kano.

Dala FM Kano 88.5 FM
Dala FM Kano 88.5 FM · Kai tsaye
Live