Siyasa
Kwankwaso ya zargi Gwamna Abba da amfani da hukumomin yaƙi cin hanci da rashawa wajen yaƙar sa a siyasance.

Tsohon Gwamnan Kano, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso, ya zargi Gwamna Abba Kabir Yusuf da ƙoƙarin amfani da hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa wajen yaƙar sa a siyasance, da nufin ɓata masa suna da raunana damar tafiyar siyasarsa a zaɓen 2027.
Kwankwaso ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na Facebook, ya ce Gwamna Abba, wanda ya taɓa yi masa aiki a matsayin mai taimaka masa na musamman, (Principal Private Secretary) da kuma kwamishina, ya yi amfani da amana da dangantakar da ke tsakaninsu ta tsawon shekaru 43.
Ya kuma zargi gwamnan da ƙoƙarin shigar da shi da iyalinsa cikin rikicin siyasa ta hanyar amfani da hukumomi.
A cikin sanarwar, Kwankwaso ya yi zargin cewa gwamnan ya gabatar da buƙata ga EFCC domin a bincike shi, amma bayan hakan ya kasa samun nasara, sai aka yi amfani da wata ƙungiya mai suna Society for Anti-Corruption and Good Governance Initiative (SACGGI) wajen shirya zanga-zanga a ofishin EFCC.
Ya kuma zargi wasu jami’an gwamnati da yaɗa bayanai ga kafafen yaɗa labarai domin ƙara ɓata masa suna, tare da yunƙurin kawo cikas ga takarar Kwamared Aminu Abdussalam a 2027.
Kwankwaso ya bayyana godiyarsa ga EFCC bisa yadda ta gudanar da gayyatar da ta taɓa yi masa a baya, yana mai cewa ya bar gwamnatin Kano sama da shekaru 11 da suka wuce ba tare da wani zargi da ya tabbatar da rashin gaskiyarsa ba.
Ya kuma yi kira ga ’yan siyasa da masu riƙe da mukaman gwamnati da su mutunta ’yancin hukumomi, su guji ayyukan da za su raunana amincewar jama’a ga hukumomin ƙasa.


